1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bore har sai an ga abin da ya ture wa Buzu nadi

July 29, 2013

A daidai lokacin da sabbin mahukuntan Masar ke dawo da wani bangare na dokar ta-baci, masu adawa da juyin mulki sun sha alwashin ci gaba da fafutuka cikin lumana.

https://p.dw.com/p/19Gmh
Supporters of deposed Egyptian President Mohamed Mursi shout slogans during a protest at the Rabaa Adawiya square, where they are camping, in Cairo July 27, 2013. At least 70 people died on Saturday after security forces attacked supporters of deposed President Mohamed Mursi in Cairo, Muslim Brotherhood spokesman Gehad El-Haddad said, adding the toll could be much higher. REUTERS/Mohamed Abd El Ghany (EGYPT - Tags: POLITICS CIVIL UNREST)
Hoto: Reuters/Mohamed Abd El Ghany

Kwanaki biyu bayan wani kisan kiyashi da jami'an tsaron Masar gami da 'yan banga suka yi wa masu zaman dirshan dake neman dawo da Muhammed Mursi kan karagar mulki, gamayyar masu adawa da juyin mulki a kasar, ta yi kira ga 'yan kasar da su fita kwansu da kwarkwatarsu, dauke da makaru da likkafanai, a wannan Litinin bayan shan ruwa, zuwa ofisoshin 'yan sanda a duk fadin kasar, don yin tofin Allah tsine da murkushe zanga-zangar nuna kin jinin juyin mulki da jami'an tsaron suka yi, ta yin amfani da albarusai masu kisa, da kuma ci gaba da kamewa da tsarewa da jami'an tsaron suke wa masu adawa da juyin mulkin. Muhammad Baltaji kusa ne a kungiyar 'Yan uwa Musulmi da suka gayyaci yin jerin gwanon.

"Ba za ma taba barin mulkin kama karya ya dawo kasar nan ba, sai a bakin ranmu. Mursi shi ne madugun juyin juya hali da talakawa suka zaba, kuma duk muna bayansa don hana mulkin daure-daure da kashe-kashen mutane ya sake bararrajewa a kasar nan."

Dawo da wani bangare na dokar ta-baci

Anti-Mursi protesters carry posters of army chief Abdel-Fattah El-Sisi as they chant slogans during a mass protest to support the army in Tahrir square, Cairo, July 26, 2013. Many of those Egyptians opposed to ousted President Mohamed Mursi say their admiration for the army has never wavered, and that any anger was always directed at the generals in charge. In the turbulent world of Egyptian politics since Hosni Mubarak, a former air force marshal, was toppled, the military is seen as an institution that offers stability. REUTERS/Asmaa Waguih (EGYPT - Tags: POLITICS CIVIL UNREST)
Magoya bayan juyin mulki a dandalin TahrirHoto: Reuters

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban rikon kwaryar kasar Adli Mansur ya ba wa Firaminista Hazim Al-Bablawi ikon yin amfani da wani bangare na dokar ta-baci wajen dawo da doka da oda a kasar, dokar da aka soke aiki da ita shekarar da ta gabata. Dokar dai ta yi kaurin suna wajen keta hurumi da hakkin dan Adam da shugabannin kama karya na kasar suka yi kusan shekaru 60 suna aiki da ita. Suna murkushe 'yan adawa da masu tsattsauran ra'ayin Islama ba tare da an gabatar da su gaban kotu ba. Daga baya dai ta yi sanadiyar barkewar zanga-zangar da ta kai ga yin juyin juya halin da ya hambarar da Hosni Mubarak.

A ranar Asabar din din da ta gabata dai ministan cikin gidan Masar Muhammad Ibrahim, ya yi barazanar fasa zaman dirshan din da magoya bayan Mursi ke yi ta yin amfani da karfin doka.

A daura da haka, wasu dake kiran kansu jagororin juyin juya hali, sun fara yin kiraye-kiraye ta gidan Telebijin kasar ga babban kwamandan sojin kasar Abdulfattah Alsisi da ya tsaya takarar shugaban kasa.

Egypt's interim President Adli Mansour (R) meets with EU foreign policy chief Catherine Ashton at El-Thadiya presidential palace in Cairo July 29, 2013. Ashton became the first senior overseas envoy to visit Egypt's new rulers since the weekend killing of at least 80 supporters of the country's deposed Islamist president. REUTERS/Amr Abdallah Dalsh (EGYPT - Tags: POLITICS)
Ashton da shugaban rikon kwarya Adli MansourHoto: Reuters/Amr Abdallah Dalsh

Kokarin samun mafita a diplomasiyance

A ta bangaren diplomasiyya kuwa, tawagar Tarayyar Afirka da ta ziyarci kasar don gane wa idonta abin dake gudana a kasa, ta yi kira ga illahirin bangarorin kasar da su bi hanyar tattaunawa don fita daga yamutsin siyasar da ya kara kazanta bayan kawar da Mursi.

Haka nan ita ma, babbar jami'ar Diplomasiyar kungiyar Tarayyar Turai Catherine Ashton, na ci gaba da ganawa da sabbin mahukuntan na Masar, kamar yadda take shirin ganawa da wakilan gamayyar masu nuna kin jinin juyin mulki. Kakakin gwamnatin rikon kwaryar, Ahmad Almusalmani, ya musanta jita-jitar da ake na shirin ganawar jami'ar tarayyar Turan da tsararren shugaba Mursi, yana mai cewa, hambararran shugaban mai laifi ne ba fursinan siyasa ba.

Mawallafi: Mahmud Yaya Azare
Edita: Mohammad Nasiru Awal