Bore Fursunoni a gidan kurkuku a Mexiko | Labarai | DW | 11.02.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bore Fursunoni a gidan kurkuku a Mexiko

Hukumomi ƙasar Mexiko sun ce fursunoni 52 suka mutu a sa'ilin da wani bore ya arke a cikin wani gidan kurkuku na Monterey da ke a yankin arewa maso gabashi na ƙasar

Gwamnan jihar ta Nuevo Leon,Jaime Rodriguez ya ce fursunonin na gidan kurkukun Topo Chiko na jihar ta Nuevo tun da safe suka soma yin boren.

Dangui da 'yan uwan 'yan kaso sun yi cirko-cirko a gaban gidan kurkukun wanda 'yan sanda suka yi masa zobe suna jifarsu da duwarwatsu.Sotari dai a kan samu bore a cikin gidajen kurkuku da ke da cikonso 'yan kaso galibi dilalai miyagun ƙwayoyi a ƙasar ta Mexiko.