Boran sojoji a Cote d′Ivoire | Labarai | DW | 06.01.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Boran sojoji a Cote d'Ivoire

Tsofin 'yan tawaye wadanda suka goyi bayan Alassane Ouattara wadanda aka saka cikin rundunar sojojin kasar na yin zanga-zanga.

An ba da rahoton cewar an ji duriyar manyan makamai a birnin na biyu mafi girma na Cote d'Ivoire watau Bouake a kusa da barakin sojoji.Masu aiko da rahotanni sun ce tsofin sojojin wadanda suka ce suna bukatar ko wane a bashi kusan Euro dubu bakwai da rabi na kudaden alawus da kuma gidan kwana,sun kai farmaki a kan wasu ofisoshin 'yan sanda guda biyu inda suka amshe makamai daga 'yan sandar wadanda suka tafi da su.