Bookboon kafar samar da littattafai ta intanet | Zamantakewa | DW | 10.08.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Bookboon kafar samar da littattafai ta intanet

Don ganin an samu sauki musamman a fannin littattafan karatu, wani kamfanin kasar Denmark mai suna Bookboon ya fara samar da littattafai kyauta ta hanyar intanet

Don ganin an samu sauki musamman a fannin littattafan karatu, wani kamfanin kasar Denmark mai suna Bookboon ya fara samar da littattafai kyauta ta hanyar intanet. Wannan na zama gagarumin taimako ga dalibai, sai dai ba zai warware matsalar tabarbarewar harkar ilimi a Afirka ba.

Shekaru biyu da suka wuce Abdul Karim dalibi dan shekaru 22 da haihuwa a kasar Ghana ya shiga neman littattafai a fannin fasahar sadarwa, amma bukata ba ta biya ba kasancewa a shagunan sayar da littattafai a Ghana ba su da irin wadanda dalibai ke bukata, imma akwai to suna da tsadar gaske. Haka lamarin yake a ilahirin nahiyar Afirka. Albarkacin kamfanin Bookboon na kasar Denmark da ke ba da tallafin littattafan ta intanet, Abdul Karim ya samu littattafan da yake bukata.

Ra'ayin dalibin Afirka kan kamfanin Bookboon

"Abin da ya sa nake son Bookboon shi ne kana iya samun wasu littattafai kyauta, wasu kuma dole ne ka saye ko kuma nemi zama cikakken memba. Amma ina jin dadinsu domin suna ba da wasu littattafai kyauta wadanda ke da matukar tsada idan za ka saye su a nan, wasu lokutan ma ba ka samun su."

Kamfanin Bookboon da aka kafa shi a shekarar 2005 a birnin Kopenhagen na kasar Denmark na ba wa dalibai kimanin miliyan biyar a Afirka damar saukar da littattafan ta shafin intanet. A wasu kasashen Afirka yanzu littattafan ta Intanet ko kuma E-Boooks sun zama kafar neman ilimi. Alal misali a kasar Kenya kimanin kashi 73 cikin 100 na dalibai na amfani da littattafan na E-Books, albarkacin kamfanin Bookboon. Thomas Buus Madsen shi ne shugaban kamfanin.

Ra'ayin shugaban kamfanin Bookboon kan fa'idar aikin kamfanin

"Mun saukaka hanyar samun littattafan ta intanet duk da rashin ingancin hanyoyin intanet a wasu yankunan na Afirka. Muna ba da damar saukar da littattafan a kuma adana su a komfuta ta yadda za a iya amfani da su a duk lokacin da ake so. Ba a bukatar hanyar intanet a kullum."

Sai dai dan kasar ta Denmark ya ce kamfaninsa ba kungiyar agaji ba ne, ya ce da shi da abokan aikinsa suna aiki ne don samun riba. Da kudin tallace-tallace da suke wa wasu kamfanoni da ke neman sabbin ma'aikata, suke tallafa wa wannan aiki na samar da littattafan na E-Books kyauta.

"Daga kamfanoni irin su Siemens da Skoda da muke wa talla lokacin da suke neman sabbin ma'aikata muke samun kudin gudanar da aikinmu. Muna kuma da wasu jami'o'i da ke tallafa mana."

Duk da wannan kokarin da kamfanin na Bookboon ke yi, Abdul Karim daga kasar Ghana ya ce da sauran rina a kaba domin ba kowane littafi ne kamfanin ke iya samarwa ba.