1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bom ya kashe sojojin kasar Mali

September 28, 2018

Wata nakiya ta yi sanadin wasu sojojin Mali tare da matukinsu a tsakiyar kasar, kamar yadda hukumomi suka tabbatar.

https://p.dw.com/p/35c0F
Unruhe in Mali
Hoto: Getty Images/Stringer

Hukumomi a Mali sun tabbatar da mutuwar wasu sojojin kasar bakwai da wani direba farar hula guda, bayan wani tuntube da suka yi da wata nakiya a yankin tsakiyar kasar da ke fama da hare-haren ta'addanci.

Al'amarin da aka ruwaito shi a ranar Alhamis, ya faru ne a arewacin birnin Timbuktu da kuma Mopti, lokacin da sojojin ke rakiyar wani ayari.

A ranar ta Alhamis ne kuma wasu dakarun Faransa 120 suka dira a yankin arewa maso gabashin Malin mai makwabtaka da Jamhuriyar Nijar, don yaki da ayyukan 'yan ta'addan.

Dakarun na Faransa dai sun ce suna shirin ba da mamaki ne a yankin, ta hanyar gama karfi don yaki da masu ayyukan na tarzoma.