Boko Haram ta yanka manoma a Borno | Labarai | DW | 20.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Boko Haram ta yanka manoma a Borno

Mayakan Boko Haram sun kashe mutane shida ta hanyar yi masu yankan rago, a kauyen Dimge 'yan tazarar da Maiduguri fadar gwamnatin jihar Borno.

Wasu mazauna wajen birnin Maiduguri a Najeriya

Wasu mazauna wajen birnin Maiduguri a Najeriya

Wasu da ake zargin mayakan Boko Haram ne sun kashe mutane shida ta hanyar yi masu yankan rago, a kauyen Dimge 'yar tazara da birnin Maiduguri fadar gwamnatin jihar Borno. Lamarin ya faru ne a jiya Lahadi,  yayinda manoman ke aiki a gonakinsu.

Maharan na Boko Haram su bakwai bisa babura sun sun afka wa manoman ne, sannnan suka kyale wani dattijo don ya kai labari, kamar yadda wani dan kato-da-gora ya tabbatar. Wannan hari ya tayar da hankulan manoma da suka kauracewa gonakinsu, kamar yadda 'yan uwan wadanda aka yanka suka bayyana.

Ya zuwa yanu dai jami'an tsaro ba su ce komai kan wannan hari ba, kuma ba a kaiga daukar gawarwakin mamatan ba.