Boko Haram ta sake kai hari garin Damboa | Labarai | DW | 18.07.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Boko Haram ta sake kai hari garin Damboa

Wasu ‘yan bindiga da ake zaton ‘yan kungiyar Boko Haram ne sun sake afkawa garin Damboa yau Juma'a da safe inda suka hallaka mutane da dama tare da kona gidaje masu yawa.

Wani mazauanin garin ya shaidawa wakilinmu na Gombe Al-Amin Sulaiman Muhammad cewar tun da milaslin karfe biyar na asuba ne ‘yan bindigar suka afkawa garin inda suka bude wuta kan mai uwa da wabi har ma suka a hallaka mutane da dama da kone gidaje masu tarin yawa.

Wakilin namu ya ce a garin na Damboa babu sauran jami'an tsaron tun wasu jerin hare-hare da aka kai makonni biyu da suka shude inda aka bar matasan nan 'yan kato da gora da ake fi sani da Civilian JTF da kare rayukan al'umma kamar yadda mazauna garin suka bayyana.

Ya zuwa yanzu dai babu alkaluma a hukumance da aka samu na yawan suka mutu a harin. Sai dai wani da ya tsira daga harin ya ce sun gudu sun bar gawawaki da dama a cikin gari.

Mawallafi: Al-Amin Sulaiman Muhammad
Edita: Mouhamdou Awal/Ahmed Salisu