1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Boko Haram ta kwace sansanin soji a Borno

Abdul-raheem Hassan MAB
May 4, 2019

Shaidu sun gaya wa kamfanin dillancin labaraun Faransa na AFP cewa mahara a kan babura sun kai wa sojojin hari a sansaninsu da ke garin Magumeri mai tazarar kilomita 50 da birnin Maiduguri.

https://p.dw.com/p/3Hw6G
Niger Soldaten
Hoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

Rahotanni da ke fitowa daga Arewa maso gabashin Najeriya na cewa mayakan Boko Haram sun kwace wani sansanin dakarun kasar a jihar Borno. Harin ya faru kwana guda bayan wani hari da ya yi sanadiyar mutuwar sojoji biyar yayin da  wasu 30 suka bace.

Mazauna kusa da yankin da aka kai harin sun shaida wa kamfanin dillancin labaraun Faransa na AFP cewa a daren jiya Jumma'a ne maharan suka zo kan babura suka yi wa sojojin kofar rago a sansaninsu da ke garin Magumeri mai tazarar kilomita 50 da birnin Maiduguri.

Wani jami'n soji da ya nemi a sakaye sunansa ya ce mayakan sun kwace makamansu da sauran kayan yaki da ke sansanin, amma sai da aka yi ta musayar wuta tsakanisu da mayakan kamin su ci karfinsu.