Boko Haram ta kwace garuruwa a Najeriya | Labarai | DW | 04.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Boko Haram ta kwace garuruwa a Najeriya

'Yan Boko haram sun fatattaki sojoji a barikin Baga na jihar Bornon Najeriya kafin su kwace wasu garuruwa dake da iyaka da kasar Chadi.

'Yan kungiyar Boko Haram sun kai wani hari a garuruwan Najeriya dake makwabtaka da kasar Chadi, inda suka kame wani barakin sojan hadin gwiwa na kasa-da kasa da ke wannan yanki, da kuma garuruwan Kauyen Kuros, dake a nisan kilometa akalla hudu da Doron-Baga. Sannan sun kame garin Bungaram, da kuma birnin na Baga, inda hakan ya haddasa ficewar mutane masu yawan gaske daga yankin zuwa kasar Chadi.

Wannan barakin soja na MNJTF, ta kasance ne a mashigar birni na Baga, dake a nisan kilometa180 Arewa maso gabashin Maiduguri fadar gwamnatin jihar Borno. Bayan ma bata kashi na tsawon awoyi a kalla bakoye, 'yan kungiyar sun kori sojojin dake wannan baraki, wadda ta kumshi sojojin hadin gwiwa na kasashen Nijar, da Chadi, dake cikin wannan tsari na hadin gwiwar kasashe makwabtan kasar ta Najeriya masu sa ido kan harkokin 'yan kungiyar ta Boko Haram.

Kawo yanzu dai babu wani adadi da aka bayar, amma dai mazauna yankin sun ce an kashe mutane da dama tare da kona gidaje da ma shaguna.