Boko Haram ta kashe sojoji a Najeriya | Labarai | DW | 18.04.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Boko Haram ta kashe sojoji a Najeriya

Rahotannin daga Najeriya, sun tabbatar da salwantar wasu jam'ian sojin kasa a wani hari da mayakan ISWAP suka kai wa sansaninsu da ke a jihar Borno a ranar Asabar.

Wasu majiyoyin soji a Najeriya, sun ce kungiyar Boko Haram bangaren Al-Barnawi ta kashe dakarun kasar, yayin da wasu da dama suka bata a wani hari da aka kai wa sansaninsu da ke a gundumar Biu da ke cikin jihar Borno a jiya Asabar.

Wasu sojojin sun shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa cewa harin ya yi sanadin salwantar sojoji akalla biyar, wasu 58 kuwa ana ci gaba da neman su.

Lamarin ya faru ne a sansanin soja da ke kauyen Kamuya, mai nisan kilomita 35 da garin na Biu, bayan musayar wuta.

Ya zuwa yanzu akwai sojoji 41 da aka gano, yayin kuma da ake ci gaba da neman 58 din kamar yadda wasu dakarun da ba su so a bayyana sunyayensu ba suka tabbatar.

Kauyen na Kamuya dai, nan ne mahaifar tsohon babban hafsan tsaron Najeriyar, Laftanal Janar Tukur Buratai, yankin da ke fama da hare-haren 'yan bindigar da ya sanya kafa sansanin soji a yankin.

Sabon harin ya zo lokacin da dakarun na Najeriya ke kokarin dawo da zaman lafiya a yankin Arewa maso gabashin kasar, musamman da wani hari da aka kai garin Damasak a wannan makon, inda Majalisar Dinkin ta ce sama da mutum dubu 65 suka tsere wa matsugunansu suka fada Nijar.