Boko Haram ta kashe mutane 10 a Kamaru | Labarai | DW | 07.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Boko Haram ta kashe mutane 10 a Kamaru

Hukumomin ƙasar sun ce mayaƙan ƙungiyar sun kai farmaki ne a wani garin da ke a yankin arewaci a kan wata motar da ke ɗauke da fasinja.

Wani babban jami'in gwamnatin ƙasar ta Kamaru ya ce wani gungun ne, na mahaharan suka datse hanyar mota a garin Zigague. Kana suka tare wata babbar motar da ke ɗauke da farar hula guda tara da soji ɗaya waɗanda suka buɗewa wuta nan take suka hallakasu.

Wannan hari, ya biyo bayan sace mai ɗakin mataimakin firaministan ƙasar ta Kamaru, da wasu mutane 15 da Ƙungiyar Boko Haram ta yi a makon jiya a arewacin ƙasar ta Kamaru.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu