1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyar Bako Haram ta kai hari a Marte

Abdoulaye Mamane Amadou MAB
January 16, 2021

Kungiyar ISWAP mai fafutukar da'awa a yankin yammacin Afirka ta kama iko da barikin sojan Marte da ke yankin Arewa maso gabashin tarayyar Najeriya.

https://p.dw.com/p/3o0yp
Nigeria Islmischer Staat in West Afrika ISWAP Truck
Hoto: Getty Images/AFP/A. Marte

Rahotanni daga yankin sun ce an shafe tsawon yammacin ranar Jumma'a ana artabu da maharan, wadanda suka far wa sansanin sojan da muggan makama. Majiyar soji a Najeriya da ba ta so a bayyana sunanta ba ta tabbatar da harin na mayakan kungiyar Boko Haram, tare da tabbatar da cewa har yanzu kungiyar ce ke riko da iko da barikin sojan.

Wannan lamarin na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da gwabza yaki a yankin Tafkin Chadi tsakanin mayakan kungiyar da jami'an tsaro, a wani yunkuri na kawo karshen ayyukan kungiyar da suka yi sanadiyar rayukan mutane, da tilasta wa wasu kaurace wa gidajensu galibin su fararen hula.