Boko Haram ta kama mata a Nijar | Labarai | DW | 04.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Boko Haram ta kama mata a Nijar

Harin dai an kai shi ne a ranar Lahadi a kauyen na Ngalewa da ke kusa da iyaka da Najeriya kamar yadda gwamnan Diffa Laouali Mahamane Dan Dano ya bayyana haka.

Mayakan Boko Haram sun sace mata 37 da yanka makogwaro na wasu mutane a wani kauye da ke a Kudu maso Gabashi na Jamhuriyar Nijar kamar yadda gwamna a yankin ya bayyana a wannan rana ta Talata. Harin dai an kai shi ne a ranar Lahadi a  kauyen na Ngalewa da ke kusa da iyaka da Najeriya kamar yadda gwamnan Diffa Laouali Mahamane Dan Dano ya bayyana wa kafar yada labarai a jihar.

A cewar gwamnan tuni jami'an tsaro suka shiga aiki na bincike inda mayakan na Boko Haram suka tafi da matan don samar musu 'yancinsu.

A cewar magajin garin na  Ngalewa El Hadj Daouda, yayin tattaunawa da kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP  an kai hari a garin ne a ranar Lahadi da misalin karfe goma zuwa sha daya na dare.