Boko Haram ta kai hari a Kamaru | Labarai | DW | 25.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Boko Haram ta kai hari a Kamaru

Hukumomi a Jamhuriyar Kamaru sun ce mayakan Boko Haram sun halaka mutane 11 tare da yin garkuwa da wasu 8 a yankin arewacin kasar.

Mayakan na Boko Haram sun kaddamar da harin ne a cikin daren da ya gabata a kauyen Gakara da ke a kan iyakar Kamarun da Najeriya, bayanai daga bakin mazauna yankin da lamarin ya faru na cewa maharan sun kona gidaje kimanin 30 a wannan harin.

Majiya daga ma'aikatar tsaron kasar na cewa mayakan da ake zargi 'yan  kungiyar Boko Haram ne sun halaka mutane goma sha daya a harin tare da yin garkuwa da wasu mutane takwas harin da suka kai a yankin arewacin kasar.