Boko Haram ta kai hari a gabashin kasar Nijar | Labarai | DW | 18.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Boko Haram ta kai hari a gabashin kasar Nijar

Hukumomin tsaro a Jamhuriyar Nijar sun tabbatar da wani hari da 'yan kungiyar Boko Haram suka kai a wasu garuruwa guda biyu na jihar Diffa da ke gabashin kasar.

Rahotanni daga Jamhuiriyar Nijar na cewa 'yan kungiyar Boko Haram sun kai hari a daren Laraba a wasu garuruwa guda biyu da ke cikin jihar Diffa a gabashin kasar ta Nijar, inda suka kashe mutane akalla 30. Wannan dai shi ne karo na biyu da 'yan kungiyar ta Boko Haram ke kai hari a wajan kasar Najeriya cikin mako guda, bayan harin da suka kai a ranar Litinin a birnin Ndjamena na kasar Chadi, wanda ya yi sanadiyyar rasuwar mutane 34.