Boko Haram ta kai hare-hare a Borno Najeriya | Labarai | DW | 25.03.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Boko Haram ta kai hare-hare a Borno Najeriya

Harin ya rutsa da 'yan sanda da kuma farar hula a birnin Maiduguri fadar gwamnatin jihar.

An ba da rahoton cewar mutane aƙalla guda takwas suka mutu a cikin jerin wasu hare-hare guda biyu da aka kai a birnin Maiduguri fadar gwamnatin jihar Borno da ke a yakin arewa maso gabashin Tarayyar Najeriya. Wani kakakin ‘yan sanda na jihar Gidon Jibrin ya shaidawa manema labarai cewar da farko wata motar da ke cikin tafiya ta yi bindiga ta kashe matuƙinta da wasu farar hula guda uku da ke kusa da motar. Ya kuma ce an shirya kai harin ƙunar baƙin wake ne da motar da ke maƙare da bama-bamai a wani wurin amma bam ɗin ta fashe kafin motar ta isa a wurin.

Sannan mintoci goma bayan haka aka kai wani harin a wani wurin binciken ababen hawa wanda a ciki ‘yan sanda biyar suka mutu tare da maharan guda uku a unguwar Dalori. Hukumomin jihar na Borno sun ɗora alhakin hare-haren a kan Ƙungiyar Boko Haram sai dai har yanzu ƙungiyar ba ta ce ufan ba.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Zainab Mohammed Abubakar