Boko Haram ta kai farmaki a kusa da Borno | Labarai | DW | 09.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Boko Haram ta kai farmaki a kusa da Borno

A cewar wasu da sanyin safiyar Talatan nan ce ‘yan bindigar suka fice daga kauyen Huyum da ke yankin karamar hukumar Askira Uba a jihar Borno bayan da suka kona daukacin gidajen garin Kurmus.

Wasu ‘yan bindiga da ake zaton ‘yan Kungiyar Boko Haram ne sun hallaka mutane 14 tare da jikkata wasu da dama a kauyen Huyum da ke yankin karamar hukumar Askira Uba a jihar Borno bayan wasu jerin hare-haren da suka kai jiya.

Al’ummar garin da ke da sauran shan ruwa da suka tsere zuwa garin Askira sun bayyanacewa da misalin karfe biyu na ranar jiya ‘yan bindigar suka afkawa garin inda inda su ka yi ta harbi na kan mai uwa da wabi tare da cinna wuta a gidajen garin.

A cewar wasu sai da sanyin safiyar Talata ne ‘yan bindigar suka fice daga garin bayan da suka kona daukacin gidajen garin kurmus. Haka kuma sun bayyana cewa ‘yan bindigar sun kona kauyuka da ke makobtaka da garin na Huyum inda suka ce babu wani dauki da suka samu da jami’an tsaro duk da cewa sun sanar da hukumomi abinda ke faruwa.

Ya zuwa yanzu dai mafarauta sun watsu cikin jeji don nemo mutane da suka nemi tsira ko a same su da sauran numfashi.

Hukumomi da jami’an tsaro ba su kai ga cewa komai ba kan wannan sabon hari .