1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Boko Haram ta halaka rayuka a Najeriya

July 19, 2018

Wani harin kwanton-bauna da Boko Haram ta kai kan matafiya, ya yi sanadiyar mutuwar mutane a jihar Borno ta Najeriya.

https://p.dw.com/p/31kyf
Boko Haram
Hoto: Java

Kimanin mutane bakwai ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu da dama kuwa suka jikkata a wani hari da ake zargin mayakan Boko Haram ne suka kai kan wasu matafiya a kan hanyar Gamboru Ngala zuwa garin Dikwa a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Lamarin da ya faru a ranar Talata da ta gabata, shaidun sun ce maharan sun yi wa matafiyan kwanton-bauna ne suka kuma buda musu wuta, akwai kuma wadanda suka tsira ba tare da samun rauni ba.

An dai yi jinkirin samun labarin ne saboda rashin hanyoyin sadarwa a yankin da abin ya faru

Mayakan na Boko Haram sun kona motocin matafiyan guda shida kurmus, an kuma ruwaito cewa sun kwashi kayayyakin abinci da ke cikin motocin. Hukumomi dai ba su ce komai ba kan wannan hari.