Boko Haram ta halaka rayuka a Najeriya | Labarai | DW | 25.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Boko Haram ta halaka rayuka a Najeriya

Wani harin kwanton bauna na tsagerun kungiyar Boko Haram masu dauke da makamai ya janyo mutuwar mutane biyar a yankin arewa maso gabashin Najeriya.

An tabbatar da mutuwar mutane biyar a harin kwanton bauna da ake zargin mayakan kungiyar Boko Harama da kai wa a  jahar Borno da ke a arewa maso gabashin kasar, an kai harin ne a wannan Alhamis akan ayarin motocin sojoji da ke samun rakiyar jami'an sa-kai na kato da gora a kauyen Meleri na karamar hukumar Konduga, mayakan sa kan hudu da direban motar guda ne suka rasa rayukansu a cewar shugaban 'yan kato da gora na wannan yankin.