1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Boko Haram ta fitar da sabon bidiyo

May 12, 2014

Ƙungiyar Jama’atu Ahlul Sunna Lidda’awati Wal Jihad wacce ake kira da sunan Boko Haram ta fitar da sabon bidiyo inda ta nuna 'yan mata 'yan makaranta da ta sace,a garin Chibok da ke cikin jihar Borno a Najeriya.

https://p.dw.com/p/1ByVH
Boko Haram Video 12.5.2014
Hoto: picture alliance/abaca

Shugaban ƙungiyar Imam Abubakar Shekau wanda ya yi wasu jawabai a sabon faifayi na bidiyon ya nuna 'yan mata da dama sanye da hijabai a wani daji wanda a nan ne ake zaton ana tsare da su. Shugaban dai ya gindaya sharuɗa na cewar in har ana so su saki ‘yan matan da ke hannun su, to ya zama dole a sake musu ‘yan uwa maza da mata da yanzu haka ke tsare a wurare daban-daban a Najeriya .

Ƙungiyar ta dage cewar ba za ta sako 'yan matan ba

Ƙungiyar ta kuma bayyana cewar yawancin ‘yan matan sun shiga musulunci inda akwai waɗanda ba su shiga ba kuma ta na a kan bakanta na cewa ta kame su ne a matsayin bayi kuma za ta sayar da su ko kuma yi musu aure kamar yadda ta bayyana a baya. An dai nuwa waɗannan‘yan mata da aka kame sama da makonnin huɗu a makarantar sakandare da ke garin Chibok sanye da hijabi inda wasu ke tsaye wasu kuma suna zaune kuma an nuna su suna karatu.Uku daga cikin ‘yan matan sun yi jawabi na nuna halin da suke ciki

Boko-Haram-Chef Abubakar Shekau BITTE BESCHREIBUNG BEACHTEN / SCHLECHTE QUALITÄT
Hoto: picture-alliance/dpa

Malam Adamu Adamu Mai Dala wani mai fashin baki ne kan harkokin yau da kullum a Najeriya. Ya ce:'' Abin da jama'a ke buƙata shi ne cewar a sako 'yan matan da gaggawa, ba tare da ɓata lokaci ba.''

Daga ƙasa za a iya sauraron wannan rahoto haɗe da martanin da wakilanmu na Lagas da Abuja da Yola suka aiko mana a kan batun

Mawallafi : Muhammad Al-Amin
Edita : Abdourahamane Hassane