Boko Haram ta ayyana kafa daula | Labarai | DW | 24.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Boko Haram ta ayyana kafa daula

Tsagerun Ƙungiyar Boko Haram masu ɗauke da makamai sun bayyana kafa daular Islama a wasu yankunan arewacin Najeriya.

Ƙungiyar Boko Haram ta ayyana kafa sabuwar daular Musulunci a garin Gwoza da ke jihar Borno Arewa maso gabashin Najeriya. A wani sabon sako na faifayin bidiyo da ƙungiyar ta fitar shugaban tsagerun ƙungiyar Abubakar Shekau ya ce sun kafa daula a wannan yanki da ke ƙarƙashin ikonsu bayan da suka karɓi iko da shi makonni uku da suka wuce.

Shugaban wanda ya yi bayani tsakanin kwamandojinsa da ke tsaye gaban wasu manyan motoci, ya yi jawabi ne cikin harsunan Hausa da Larabci inda ya nuna irin nasarar da ƙungiyar ke samu a yaƙin da suke yi da jami'an tsaron Najeriya. Ya zuwa yanzu dai gwamnatin Najeriya ba ta ce komai ba a kan wannan iƙirari da Ƙungiyar Boko Haram ta fitar, wanda ke zuwa dai dai lokacin da ake zargin ƙungiyar ita ce riƙe da iko da wasu sassan kudancin jihar Borno.

Mawallafi: Amin Suleiman Mohammad
Edita: Abdourahamane Hassane