Boko Haram ta aura wa kanta sama da 'yan matan Chibok 20 | Labarai | DW | 22.06.2022
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Boko Haram ta aura wa kanta sama da 'yan matan Chibok 20

'Yan matan Chibok biyu da sojoji suka ceto ne suka shaida wa 'yan jarida yadda Boko Haram ta yi musu auran dole. A cikin daji ne dai sojojin suka samu matan, kowacce da karamin yaron da ta haifa wa dan Boko Haram.

Rundunar sojin Najeriya ta gano tsaffin dalibai mata na makarantar sakandaren Chibok ta jihar Borno da ke cikin 'yan mata 276 da kungiyar Boko Haram ta kwase shekaru takwas da suka gabata. 


A yayin da yake gabatar da matan a Maiduguri, Manjo Janar Christopher Musa, wani babban jami'in sojin Najeriya  ya ce a wurare dabam-dabam sojoji suka yi nasarar samun matan a makon da ya gabata. 


Mary Dauda da sojojin suka gan ta a cikin daji ta ce kawo yanzu Boko Haram ta aura wa mambobinta sama da matan Chibok 20 da ta baro. Ta ce mayakan Boko Haram kan lakada musu duka idan ba su yi sallah ba. Ita kuma Hauwa Joseph ta ce dan Boko Haram din da ya aure ta ya mutu a yayin wani gumurzu da sojojin Najeriya. Ta ce bayan mutuwarsa mambobin kungiyar sun yi watsi da ita da karamin yaron da ta haifa.