Boko Haram: Soji sun shiga dajin Sambisa | Labarai | DW | 22.04.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Boko Haram: Soji sun shiga dajin Sambisa

Dakarun Najeriya sun kutsa dajin nan na Sambisa a wani abin da sojin ke cewa fafatawa ce ta karshe da suke sa ran yi da 'yan kungiyar Boko Haram.

Dakarun na Najeriya na kasa da ma mayakan sama, su ne dai rahotannin suka tabbatar da dannawarsu cikin dajin a Larabar ta yau.

Sai dai ya zuwa wannan lokacin babu wani sakamako dangane da dauki-ba-dadin da ya wakana a arangamar da ake ganin za ta hada da kubuto da 'yan matan makarantar Chibok sama da 200 da ke hannun mayakan yau sama da shekara guda kenan.

A watannin baya ma dai sojojin Kamaru da Chadi da ma Jamhuriyar Nijar, sun zafafa hare-hare kan mayakan na Boko Haram, a kokarin murkushe su saboda fadada hare-hare da kungiyar ta yi zuwa ketaren Najeriyar.