Boko Haram na kashe mutane a Gamboru Ngala | Labarai | DW | 31.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Boko Haram na kashe mutane a Gamboru Ngala

'Yan kungiyar Boko Haram da suka kwaci garin Gamboru Ngala dake iyaka da kasar Kamarun, na ci gaba da kashe-kashen mutane a wannan gari.

A cewar wani mazaunin garin mai suna Sidi Kyarimi, da a halin yanzu ya gudu zuwa garin Fotokol dake kasar Kamarun, 'yan kungiyar ta Boko Haram na kashe mutane tamkar suka kisan kaji, inda yace sun fara ne zabar mutanan da suke kashewa kafin daga bisani su koma ga kisan kare dangi.

A cewar wannan majiya dai, daga cikin wadanda aka kashe har da manyan Limamman garin, da kuma duk wanda bai gudu ba, inda a cewar sa 'yan kungiyar ta Boko Haram sunce mazauna garin da su fice daga garin tunda ba garin su ne ba, kuma suna bi layi-layi ne na cikin garin dauke da bindigogi, da adduna a cewar Yussuf Sanda shima wani mazaunin garin da yayi gudun hijira. A kalla dai 'yan kungiyar ta Boko Haram na rike da wurare da dama na jihar Borno a da suka kwata daga hannun dakarun gwamnatin kasar.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Umaru ALiyu