1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Boko Haram: Da sauran rina a kaba

May 14, 2019

Wasu kwamandojin yaki na sojojin Najeriya da wasu dakaru biyu sun rasa rayukansu, bayan da motarsu ta taka wata nakiya da ake zaton mayakan Boko Haram ne su ka dasa a yankin Damboa na jihar Borno.

https://p.dw.com/p/3IURd
Kamerun Symbolbild Soldaten im Norden ARCHIV
Manyan sojojin Najeriya asun rasa ransu a wasu hare-haren Boko HaramHoto: Getty Images/AFP/R. Kaze

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da wani dan kunar bakin wake da ake zaton kungiyar Boko Haram da ke da alaka da kungiyar ISIS ce ta tura shi, ya tada bam da ke daure a jikinsa a wani sansanin sojojin da ke Barkoza Dalori a karamar hukumar Kaga cikin jihar ta Borno, inda nan ma wani kwamandan mai mukamin Laftanar Kanar ya rasa ransa. Kwamandan na farko dai ya bi ta kan nakiya ne da aka dasa akan hanya yayin da ya ke jagorantar wata rundunar sojoji mai yin sintiri a yankin Damboa kuma nan take ya rasa ransa kamar yadda shaidun gani da ido su ka tabbatar. Bayan kwamandan sojojin mai mukamin Laftanar Kanar da wasu dakarunsa biyu da suka mutu wasu Sojoji guda hudu sun samu munanan raunuka, inda aka garzaya da su Maiduguri fadar gwamnatin jihar ta Borno cikin jirgin sama mai saukar ungulu domin samun kulawar likitoci. Malam Abdul’Aziz Mala wani jami'in aikin jin kai ne dai ya tabbatar wa da DW hare-haren guda biyu.


Ya zuwa lokacin hada rahoton dai, gwamnati ko rundunar sojojin ba su ce komai kan mutuwar manyan kwamandojin biyu ba balle su ayyana sunayensu. Mazauna birnin Maiduguri sun shaida ganin karuwar jiragen yaki da shawaginsu a sararin samaniyar garin wanda ba a saba gani ba, abinda ya ke tada hankulan mazauna birnin da kauyukan da ke kusa. Yanzu haka daruruwan mutane na gudu daga garuruwansu zuwa Maiduguri, domin tsira daga barazanar hare-haren mayakan Boko Haram din da su ka ce suna fuskanta duk da jami’an tsaron da ke jibge a yankunan nasu. Firgicin da mutanen suka shiga dai na zuwa ne a daidai lokacin da mataimakin shugaban Najeriyar Farfesa Yemi Osinbajo ya tabbatar da cewa mayakan Boko Haram na iko da wasu yankuna a jihar Borno, ta yadda jami'an kiwon lafiya da masu kai kayan agaji ba sa iya isa ga al'ummar da yanzu haka su ke tserewa. Wannan dai shi ne karo na farko da wani banna jami'in gwamnati ya fito ya ke bayyana wanzuwar mayakan Boko Haram a sassan Arewa maso Gabashin Najeriyar, bayan da a baya hukumomi ke ikirarin cewa ba inda mayakan suka kame. Mayakan na Boko Haram dai, na zafafa hare-haren da suke kai wa a jihohin Borno da Yobe, abin da ya yi sanadiyyar mutuwar fararen hula da kuma tilasta mutane tserewa daga garuruwansu.

Mutmaßlicher Boko-Haram-Angriff in Nigeria
Boko Haram na ci gaba da zafafa kai hare-hare a NajeriyaHoto: picture-alliance/AP/Jossy Ola