Boko Haram da AFCON a jaridun Jamus | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 16.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Boko Haram da AFCON a jaridun Jamus

Kusan ko wace jarida a nan Jamus cikin wannan mako ta duba halin da ake ciki na aiyukan kungiyar Boko Haram a Najeriya, sai kuma wasannin AFCON a Equatoial Guinea

Jaridar Die Welt tayi magana game da hotunan taurarin dan Adam da suka nuna irin barnar da mayakan kungiyar Boko Haram suka yi a garin Baga na jihar Borno, inda ake cewar mutanen da suka kashe sun kai dubu biyu, tare da lalata gidaje fie da 3000. Jaridar ta ambaci rahoton kungiyar Amnesty International, inda tace wadanda suka tsira da rayukansu daga wannan rashin imani na Boko Haram sun yi korafin yadda jami'an tsaro suka kasa basu kariya ko taimako a daidai lokacin da suke bukatar taimakon. A daura da haka, gwamnati da jami'an tsaron suna maimaita cewar yawan wadanda aka kashe a garin na Baga basu wuce 150 ba.

Ita ma jaridar Frankfurter Allgemeine Zaitung tace wata guda kafin zabubbuka a Najeriya, cikin watan Fabrairu, kungiyar Boko Haram bata nuna alamun sassautawa ba a aiyukanta na rashin imani kan al'ummar arewacin kasar. Jaridar tace makon jiya dai shine mafi muni na hare-haren kungiyar ta Boko Haram, inda a garin Baga mayakanta suka halaka fiye da mutane 2000, a kusa da tafkin Chadi dake iyakar kasar da jamhuriyar Nijar, inda aka taba samun sansanin sojojin hadin gwiwa na Chadi da Najeriya da Nijar, domin yaki da kungiyar. A daidai lokacin da kungiyar ta Boko Haram take kara tsananta hare-harenta na kisan jama'a, shugaban kasa, Goodluck Jonathan yana can yana kampe na neman a sake zabensa kan wannan mukami, inji jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung, ko da shike ranar Alhamis, shugaban kasar ya katse kampe dinsa, inda ya ziyarci birnin Maiduguri na dan gajern lokaci.

Jaridar Berliner Zeitung dake sharhi kan halin da ake ciki a Najeriya, ta ambaci wata hira da Archbishop Ignatius Kaigama na Najeriya yayi da BBC, inda yace ya ga yadda gagarumar zanga-zangar da aka yi a birnin Paris, saboda kyamar kisan gilla da yan tarzoma suka yiwa ma'aikatan mujallar nan ta Charlie Hebdo, amma me ke hana shirya irin wannan gangami kan aiyukan Boko Haram a Najeriya? A bisa ta bakinsa, yankin Afirka ta yamma gaba daya yana bukatar irin wannanm maida hankali kamar irin wanda aka samu a birnin Paris, amma a maimakon haka, duniya gaba daya ta kyale al'ummar Najeriya da Nijar da Chadi da sauran Afirka ta yamma su san yadda zasu yi da wannan tashin hankali na yan tarzoma da kansu. Shima Simon Allison na mujallar Intrnet Daily Maverick yace kisan gilla da aka yi a Paris babu shakka mummunan abu ne, amma bai kai ko ina ba, idan aka kwatanta shi da munin kashe-kashe na dubban jama'a a Afirka ta yamma a baya-bayan nan.

Africa Cup Fans

Magoya bayan Kamaru a wasannin AFCON

Ranar Asabar a kasar Equatoial Guinea za'a bude bikin wasannin kwallon kafa na cin kofin Afrika. Wasannin zasu gudana a can ne bayan da Moroco a watan Nuwamba ta janye daga shirya su, saboda tsoron cutar Ebola da ta yadu a wasu kasshen Afirka ta yamma. Jaridar Süddeutsche Zeitung tace babu shakka yar karamar kasar dake karkashin mulkin kama karya, zata yi amfani da wadannan wasanni domin propagandar neman daga kima da matsayinta a idanun duniya. Jaridar tace ko da shike a lokacin da Morocco ta janye, yan makonni kalilan suka rage a fara wasnnin ranar 17 ga watan Janairu, amma ga shugaban kasa, Teodore Obiang Nguema, hakan dai ba wani abin damuwa bane, saboda ko ba komai, akalla zai yi amfani da wasannin na cin kofin Afirka domin jan hankalin duniya ga kasarsa, ko da shike tafi kusa da cibiyar cutar Ebola fiye da Morocco. Jaridar Süddeutsche Zeitung tace saboda ya nuna kansa a matsayin mai taimakawa talakawa, shugaba Obiang Nguema a bainar jama'a ya nuna tikitin da yace ya saya wa yan kasar dubu 40, domin su sami damar ganin wadannan wasanni na Afika.