Boko Haram: Birtaniya za ta kara tallafi ga Najeriya | Labarai | DW | 21.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Boko Haram: Birtaniya za ta kara tallafi ga Najeriya

Kwararru daga Birtaniya za su tallafa wajen bada ilimin kwarewar yadda za a iya gano ko an binne bama-bamai a wurare a Najeriyar.

Symbolbild Islamischer Staat und Social Media

Jami'an hadin gwiwar yaki da ta'addanci

Kasar Birtaniya za ta tallafa wa Najeriya a yakin da take yi da mayakan Boko Haram inda za ta bada horo na musamman ga dakarun kasar da ba da shawara ga dakarun sojan sama na Najeriyar, da ma kwararru da za su tallafa wajen bada ilimin kwarewar yadda za a iya gano ko an binne bama-bamai.

Michael Fallon Sakataren Tsaro na Birtaniya da yake jawabi a jihar Legas Kudu maso Yammacin Najeriya, ya ce kungiyar ta Boko Haram da ayyukan rashin imaninta ke da yawa, bayan hallaka mutane da bama-bamai ta na garkuwa da fararen hula, dan haka ya zama wajibi Birtaniya ta tallafa wa Najeriya da kwararru ta yadda za a kawo karshen ayyukan kungiyar.

Mista Fallon ya ce za a ninka dakarun da suke tallafa wa sojan na Najeriya daga 130 da ke bada horo ga takwarorinsu na Najeriya a cikin wannan shekara, inda a yanzu za su kai 300. Dubban mutane ne dai wannan kungiya ta Boko Haram ta halaka ta kuma raba wasu da dama da muhallansu a Najeriyar, inda kuma ayyukanta suka ketara kasashe makota.