Boko Haram: Amirka za ta taimaki Najeriya | BATUTUWA | DW | 12.03.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Boko Haram: Amirka za ta taimaki Najeriya

Sakataren harkokin wajen Amirka Rex Tillerson ya kammala ziyararsa ta farko a nahiyar Afirka, inda ya ce Amirkan za ta taimaki Najeriya a yakin da take da 'yan ta'addan Boko Haram.

Sakataren harkokin wajen Amirka Rex Tillerson

Sakataren harkokin wajen Amirka Rex Tillerson

A yayin da ya ke karkare ziyarar tasa a Afirka a Abuja fadar gwamnatin Tarayyar Najeriya, sakataren harkokin kasashen ketaren na Amirka Rex Tillerson ya yi tir da Allah wadai da sace 'yan matan da aka yi a makarantar sakandaren garin Dapchi da ke yankin arewa maso gabashin Najeriya cikin watan da ya gabata, tare kuma da bayyana kudirin Amirka na bayar da goyon bayanta ga Najeriya domin yakar mayakan Boko Haram da ke gwagwarmaya da makamai, ya na mai ceawa Najeriya na da goyon bayan Amirka a yakin da ta ke da 'yan ta'adda. Ya kuma ce dangane da batun kokarin ceto ragoawar 'yan matan Chibok da kuma na garin Dapchi da aka sace a baya-bayan nan, Tillerson din ya ce  Amirka zata taimaka da bayanai da ma horar da jamii’an tsaro da nufin tabbatar da gano su.

Makarantar sakandaren 'yan mata ta Dapchi, inda aka sace dalibai 'yan mata a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.

Makarantar sakandaren 'yan mata ta Dapchi, inda aka sace dalibai 'yan mata a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.

Tillerson dai ya isa birnin na Abuja ne daga N'Djamena babban birnin kasar Chadi. A baya dai an tsara zai kwana a Abuja kana ya tattauna a ranar Talata 13 ga wannan wata na Maris da muke ciki da jami'an ofishin jakadancin Amirka da ke Najeriyar, sai dai ya takaita ziyarar tasa sakamakon aiki da ya taso masa, inda zai koma Amirka da zarar ya kammala ganawa da mahukuntan Najeriyar.

Chadi za ta fita daga sahun kasashen da aka haramtawa zuwa Amiraka

A yayin ziyarar da ya kai kasar Chadi, Tillerson ya nunar da cewa Amirkan za ta yi aiki kafada da kafadda da kasar Chadi wajen yakar ayyukan ta'addanci a yankin yammacin Afirka ta kuma duba yi wuwar cire ta daga cikin jerin kasashen da ta haramtawa zuwa kasarta. Da ya ke jawabi a N'Djamena babban birnin kasar ta Chadi, Tillerson ya nunar da cewa matakin baya rasa nasaba da cigaban da aka samu ta fannin kara karfafa bincike dangane da fasfo da kuma musayar bayanai tsakanin kasashen biyu. Tillerson ya fara ziyarar ta sa ta farko ce tun daga ranar Laraba bakwai ga wannan wata na Maris da muke ciki, inda ya ziyarci kasashen Habasha da Djibouti da kuma Kenya kafin daga bisani ya karkare ziyarar ta sa da kasashen Chadi da Najeriya.

Sauti da bidiyo akan labarin