Blatter zai yar da kwallon mangwaro | Labarai | DW | 02.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Blatter zai yar da kwallon mangwaro

Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya FIFA Sepp Blatter ya bayyana aniyarsa ta yin murabus da ga mukaminsa.

Shugaban hukumar FIFA Sepp Blatter

Shugaban hukumar FIFA Sepp Blatter

Wannan dai na zuwa ne kwanaki hudu kacal bayan sake zabensa a matsayin shugaban hukumar a karo na biyar. Blatter ya bayyana hakan ne a yayin taron da hukumar ta gudanar a birnin Zurich na kasar Switzerland inda ya ce:

"Dama wannan sabon wa'adi ba ya da goyan bayan duniyar wasannin kwallon kafa ina nufin magoya baya da 'yan wasan kungiyoyin kwallon kafa dama duk masu ruwa da tsaki a harkar kwallon kamar mu da sauran mambobin FIFA."

Murabus din Blatter dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da ake fama da badakalar zargin cin hanci da karbar rashawa a hukumar, inda harma aka cafke waasu manyan mammbobin hukumar kwanaki biyu gabanin sake zabensa a matsayin shugaban na FIFA.