Bitar shekara ta Majalisar Ɗinkin Duniya | Siyasa | DW | 31.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Bitar shekara ta Majalisar Ɗinkin Duniya

A wannan shekara ta 2015 da ke shirin ƙarewa ne Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi bikin cika shekaru 70 cif da kafuwa.

Wannan kuwa ya zo a daidai lokacin da ta cimma matsaya a kan yarjejeniyar da ta shafi ɗumamar yanayi. Sai dai kuma ƙasashen duniya da dama na fama da yaƙe-yaƙe da ke haifar da 'yan gudun hijira.

Gargadin Majalisar a game da matsalolin da duniya ke fuskanta

Fiye da mutane miliyan 100 ne suka dogara kan hukumar agaji ta MDD wajen samun na sawa a bakin salati a shekara ta 2015. Hasali ma dai ba a taba samun yawan mutanen da suka ƙaurace wa matsugunansu shigen na wannan shekarar ba, tun bayan yakin duniya na biyu. Lamarin da ya sa sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki Moon ya yi hannuka mai sanda game da matsalolin da ake fuskanta shekaru 70 bayan kafa wannan hukuma.

Barayanar ta'addanci ga kasahen duniya

Sai dai kuma wannan shaguɓen bai hana fuskantar aiyyukan ta'ddanci da yaƙe-yaƙe da kuma ƙarancin abinci a wasu sassa na duniya ba. Dadin dadawa ma dai a watan Agustan 2014, Majalisar ta Ɗinkin Duniya ta samu kanta cikin wani abin kunya, inda ake zargin dakarunta na kiyaye zaman lafiya da lalata da ƙananan yara a Jamhriyar Afirka ta Tsakiya da Laberiya da kuma Haiti.Yayin da a Syriya kuwa, baya ga 'yan gudun hijira miliyan huɗu, yaƙin da ƙasar ta shafe shekaru biyar ta na fuskanta ya haddasa mutuwar mutane dubu 250. Ko da sakatare Ban Ki Moon sai da ya koka kan halin gaba kura baya siyaki da ƙasar ta samu kanta a ciki.

Sauti da bidiyo akan labarin