Bita kan zabuka a Jamhuriyar Nijar | Siyasa | DW | 23.02.2022
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Bita kan zabuka a Jamhuriyar Nijar

Hukumar Zabe mai Zaman Kanta a Jamhuriyar Nijar CENI tare da Hukumar Raya Kasashe ta Majalisar Dinkin Duniya PNUDD, sun shirya bita kan zabukan kasar da suka gabata.

Nijar I Ofishin Hukumar Zabe I Yamai

Shalkwatar Hukumar Zabe mai Zaman Kanta ta Jamhuriyar Nijar wato CENI

Sanin kowa ne dai zaben shugaban kasar da ya gudana a Jamhuriyar ta Nijar ya bar baya da kura, inda har yanzu ake jiran sakamakon karar da 'yan adawa suka shigar a gaban kotun ECOWAS ko CEDEAO. Matakin da Hukumar Zaben ta Nijar CENI ta dauka tun yanzu, na da muhimmanci ganin yadda kullum sai wuri ya kure ake tattauna muhimman batutuwa kan harkokin zabukan a Jamhuriyar Nijar. Jinkirin tattauna muhimman batutuwan dai, na haifar da babban rudani da cece-kuce a tsakanin 'yan siyasa da kungiyoyin farar hula masu sa ido kan harkokin zabe. Manyan kungiyoyi na kasa da kasa na taka rawar gani a harkokin shirya zabe a kasashe masu tasowa, a wani mataki na kamawa 'yan kasar shirya zabe mai inganci.

Nijar | Zaben Shugaban Kasa I Damagaram

Zaben da aka gudanar na baya-bayan nan dai, na cike da zarge-zargen 'yan adawa

Wannan mataki na Hukumar Raya Kasashe ta Majalisar Dinkin Duniya ta PUNDD dai, yunkuri ne da ake kira da mai zurfin idanu da wuri yake soma kuka. Zaman bitar ayyukan Hukumar Zaben kasar ta Nijar, an yi shi ne da dukka bangarori da suka hadar da wakilan kungiyoyin farar hula da 'yan siyasa da jami'an tsaro. Kuma a cewar Boukar Sabo mai kula da harkokin zabe a jam'iyyar PNDS Tarayya mai mulki a Nijar din, sun yaba da tsarin sosai. Shi kuwa Kane Kadaure Habibou mai magana da yawun gungun jam'iyyun adawa da suka marawa dan takara na bangaran adawa Alhaji mahamane Ousman baya cewa ya yi, tilas sai an sa masu kishin kasa a gaba idan ana son kaucewa duk wani cikas.

 

Sauti da bidiyo akan labarin