1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bisa Williams ta Amirka ta kai ziyara Burkina

Mouhamadou AwalNovember 8, 2014

Wata babbar jami'ar diplomasiyar Amirka ta kai ziyara Burkina faso a lokacin da ake neman wanda zai yi rikon ƙwarya.

https://p.dw.com/p/1DjLL
Burkina Faso - Oberst Isaac Zida
Hoto: ISSOUF SANOGO/AFP/Getty Images

Ƙaramar Sakatariyar harkokin wajen Amirka da ke kula da nahiyar Afirka Bisa Williams ta kai ziyarar bazata birnin Ouagadougou na Burkina Faso, kwanaki ƙalilan bayan saukar Blaise Compaore daga ƙaragar mulki ba girma ba arziki.Babbar jami'ar dipolamisiyar ta gana da shugaban mulkin sojen ƙasar Lt Co Isaac Zida

Babu dai wanda ya san adadin kwankin da jami'ar za ta shafe a Burkina Faso da kuma abin da agendarta ta kunsa. Amma dai Amirka na sahun gaba wajen matsawa sojojin lamba domin su mayar da mulki a hannun farar hula bayan da guguwar mulki ta yi awon gaba da gwamnatin Blaise Compaore.