1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Birtaniya ta jaddada aniyar inganta tsaro

Zulaiha Abubakar
July 29, 2019

Birtaniya ta shirya tsaf don jagorantar taron ministocin hukumar tsaron hadin gwiwa ta Five Eyes da suka  fito daga kasashen Birtaniya da Amirka da Kanada da Ostiriya da kuma New Zealand .

https://p.dw.com/p/3MuK8
UK Priti Patel ARCHIV
Hoto: picture alliance/AP Photo/A. Grant

Yayin taron na kwanaki biyu za a tattauna barazanar tsaro ta kakafen sadarwa da satar bayanai da kuma cin zarafin yara kanana ta hanyar yada hotunan batsa, batutuwan da taron zai fi mayar da hankali su ne lalubo hanyoyin magance hatsarin da kasashe ke fuskanta ta hanyar fasahar sadarwar.

Da yake amsa tanbayoyin manema labarai gabanin taron ministar cikin gida a Birtaniya Priti Patel ta bayyana cewar Bitaniya ce sahun gaba a tsaron kasa da kare rayuwar yara kanana, don haka ta dauki alwashin yin aiki tare da sauran cibiyoyin tsaro don tunkarar kalubalen.