Birtaniya za ta kara tallafa wa NATO | Labarai | DW | 21.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Birtaniya za ta kara tallafa wa NATO

A cewar Ministan harkokin tsaron Birtaniya Fallon, ya zama wajibi a ci gaba da tura wa shugaban kasar ta Rasha Putin sakon cewa kasashen na NATO kansu a hade yake.

Großbritannien Premierminister Cameron Immigration

Firaminista Cameron na Birtaniya

Birtaniya ta bayyana cewa a shirye take ta kara tallafin da ta ke bayarwa ga kungiyar tsaro ta NATO a kokarin samar da tsaro a yankin gabashin Turai ta hanyar kara wa'adin lokacin da dakarunta za su ci gaba da ayyukansu karkashin kungiyar.

Ministan harkokin tsaron Birtaniya Michael Fallon shi ya bayyana haka a ranar Lahadin nan.

Ana dai kara karfin sojin na kawancen NATO a yankin gabashin na Turai tun bayan zargin kasar Rasha da kokarin yin kutse a Ukraine, zargin da mahukuntan na birnin Masko ke karyatawa.

A cewar Ministan harkokin tsaron Birtaniya Fallon, ya zama wajibi a ci gaba da tura wa shugaban kasar ta Rasha Putin sakon cewa kasashen na NATO kansu a hade yake.