1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Birtaniya za ta jagoranci yaki da cin hanci

Mohammad Nasiru Awal/YBMay 12, 2016

David Cameron dai ya yi alkawarin cewa Birtaniya za ta zama kan gaba inda za ta kaddamar da wata cibiyar yaki da ci hanci ta kasa da kasa.

https://p.dw.com/p/1ImXZ
Königin Elizabeth II David Cameron Chris Grayling Justin Welby
Sarauniya Elizabeth II da David Cameron da sauran manyan bakiHoto: Getty Images/P.Hackett

A ranar Alhamis Firaministan Birtaniya David Cameron ya jagoranci wasu shugabanni da kuma jami'ai daga kasashe da dama inda suka alkawarta daukar tsauraran matakai don rage dukkan nau'o'i na cin hanci da rashawa. Shugabannin sun nunar da haka ne cikin wata sanarwar hadin gwiwa bayan wani taron koli kan yaki da cin hanci da rashawa da suka gudanar a birnin London na kasar Birtaniya.

"Cin hanci da rashawa shi ne musabbabin matsalolin mafi yawa a duniya kuma dole ne mu magance shi matukar muna son kokarinmu na kawo karshen talauci da yakar tsatsauran ra'ayin ta'addanci." Wannan kallaman dai na kunshe ne cikin sanarwar bayan taron kan yaki da annobar cin hanci da rashawa, da Firaministan Birtaniya David Cameron ya karbi bakoncinsa a birnin London.


Cameron dai ya yi alkawarin cewar Birtaniya za ta zama kan gaba inda za ta kaddamar da wata cibiyar yaki da ci hanci ta kasa da kasa wadda kuma za ta yi musayar bayanai na masu mallakar kamfanoni, sannan kuma za ta matsa lamba kan masu sayen kadarori a ketare su bayyana asalin dukiyarsu.

"Dalilin da ya sa na ga wannan batun na da muhammanci shi ne na yi imani cin hanci na zaman wata cutar daji a tsakiyar matsalolin da dama da ya zama wajibi mu magance su a wannan duniya. Idan muna son kasashe su fita daga matsalar talauci su samu wadata to dole mu yaki cin hanci."

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da kasarsa ke kan gaba a jerin kasashen Afirka masu fama da matsalar cin hanci na daga cikin shugabannin da suka halarci taron na birnin London, cewa ya yi kasashen duniya sun jima suna yi wa matsalar kallo daga bangare guda. Ya ce sun gaza wajen mayar wa kasashe masu tasowa dukiyoyinsu da aka sace kuma aka jibge a cibiyoyin kudin kasashen Yamma.

"Cin hanci daya ne daga cikin makiyan wannan zamani. Ya saba wa tabi'armu. Masu aikata shi da masu mara musu baya sun samar da wani tsari na raba dukiyar kasa tsakanin tsiraru yayin da mafi rinjaye na 'yan kasa ke cikin akubar talauci. Idan ana maganar yaki da cin hanci to abin kaico ne yadda gamaiyar kasa da kasa ta dauki lokaci mai tsawo tana yi ta kawar da ido. Dole ne mu kara kaimi mu yaki wannan mugun abu."

Ko da yake wakilai daga kasashe 40 da suka halarci taron kolin sun ce za a dauki karin matakan dakile hanyoyin boye kudade a wasu kasashe don kaurace wa biyan haraji, amma kungiyoyin yaki da cin hanci da suka yi gangami a gaban zauren taron sun nuna shakku ko kwalliya za ta biya kudin sabulu kamar yadda Maggie Murphy ta kungiyar Transparency International ta shaida wa DW.

Großbritannien London Cameron Anti-Korruptions-Konferenz
David Cameron da bakinsa a taron koli na yaki da cin hanci aLondon. John Kerry daga damansa Shugaba Buhari daga haguHoto: Reuters/D. Kitwood/Pool
Großbritannien London Cameron Kerry Anti-Korruptions-Konferenz
Cameron da Kerry a taron yaki da cin hanci na LondonHoto: Reuters/D. Kitwood/Pool