1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Birtaniya za ta fara rigakafin corona

December 2, 2020

Birtaniya ta zamo kasa ta farko da ta amince da allurar riga kafin cutar corona, inda za ta yi amfani da maganin da kamfanonin Pfizer da Biontech suka samar a fadin kasar.

https://p.dw.com/p/3m7Lc
Biontech Covid-19 Impfstoff
Hoto: NurPhoto/picture alliance

Hukumomin kasar sun ce za a fara amfani da maganin ne a makon gobe a wani abun da aka bayyana cewa gagarumar ci gaba aka samu a bangren yaki da wannan cuta ta COVID-19.

Kusan watanni 12 bayan bullar annobar daga yankin wuhan na kasar China, hukumar da ke tabbatar da sahihancin magunguna a Birtaniyar ta amince da ingancin maganin.

Tuni ma Firaminista Boris Johnson na Birtaniyar ya yaba da samun wannan labarin, inda a makon na gobe ake shirin farawa da wadanda suka fi kasancewa masu hadarin kamuwa da cutar ta corona a kasar.