1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An gano gawar 'yan China a bayan mota

Abdul-raheem Hassan
October 24, 2019

'Yan sandan Birtaniya sun tabbatar 'yan asalin kasar China ne aka samu gawarwakinsu 39 cikin wata kontena a bayan babbar mota.

https://p.dw.com/p/3RrRM
Großbritannien Grays 39 Tote in Container entdeckt
Hoto: picture-alliance/dpa/empics/S. Rousseau

Masu bincike sun ce akwai maza 31 cikin gawarwakin da kuma mata Takwas. Jami'an 'yan sanda na cigaba da tsare direban babbar motar da aka gano gawarwaki 39 domin gudanar da bincike.

Ana kyautata zaton an yi safarar mutanen ne daga tashar jiragen ruwa a kasar Beljiyam, ma'aikatar harkokin wajen China da ke Ingila ta tabbatar da labarin tare da aikewa da sakon jaje ga iyalan wadanda abin ya shafa.