Birtaniya ta zaku da ficewa daga EU | Labarai | DW | 19.10.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Birtaniya ta zaku da ficewa daga EU

Shugabanni daga EU na son gamsassun bayanai kan tsarin Birtaniya na ficewar kafin a kai ga kulle-kullen huldar kasuwanci nan da Disamba.

Shugabanni daga Kungiyar Tarayyar Turai sun fadawa Firaministar Birtaniya Theresa May a wannan Alhamis cewa muddin tana son ganin batun ficewar Birtaniya daga kungiyar yadda ta ke fata sai ta zo da gamsassun bayanai kan tsarinta na ficewar kafin a kai ga kulle-kullen huldar kasuwanci da kasarta nan da watan Disamba.

Firaminista May dai ta bayyana a wajen taron kasashe na Kungiyar EU da kiran gaggauta batun ficewar kasar ta Birtaniya tare da yin alkawarin mutunta al'ummar kasashen na EU da ke kasarta idan ta fita daga kungiyar.

Wannan dai na zama wani sabon kira na May da ke kara motsa maganar ficewar kasar tun daga watan jiya, sai dai jami'ai daga EU sun gaza gamsuwa da bayanan da May ke gabatarwa kan shirinsu na ficewar.