Birtaniya ta nemi EU ta kara wa Rasha takunkumi | Labarai | DW | 22.08.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Birtaniya ta nemi EU ta kara wa Rasha takunkumi

Mahukuntan birnin na Moscow sun ce masu iko na birnin London ba su da baki da za su tsara wa EU yadda za ta yi harkokinta.

London Downing Street Jeremy Hunt Ernennung Außenminister

Jeremy Hunt ministan harkokin wajen Birtaniya

Ministan harkokin wajen Birtaniya Jeremy Hunt, ya yi kira ga Kungiyar Tarayyar Turai ta kara yawan takunkumi ga kasar Rasha. Hunt ya bayyana haka ne a cibiyar samar da zaman lafiya da ke a birnin Washington a ranar Talata ya ce Birtaniya za ta kara jan hankalin EU ta kara matsa kaimi kan Rasha.

Ya ce ya kamata kungiyar ta tsaya kafada da kafada da Amirka kan batun takunkumai da Amirka ta kara maka wa Moscow a wannan wata. Ya kara da cewa Shugaba Vladimir Putin ya mayar da duniya wani abin tsoro musamman duba da kokari na murda harkoki na zabe a kasashen Yamma.

Sai dai a nasu bangaren mahukuntan birnin na Moscow sun ce mahukuntan na birnin London ba su da baki da za su tsara wa EU yadda za ta yi harkokinta kasancewar watanni kadan suka rage a cika kammala shirin ficewar Birtaniya daga kungiyar.