1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Birtaniya ta fice daga kungiyar tarayyar Turai

Zulaiha Abubakar
February 1, 2020

A ranar Jumma'a (31.01.2020) ne Birtaniya ta fice daga kungiyar Tarayyar Turai, wasu daga cikin al'ummar kasar dai sun bayyana fargaba game makomar kasar bayan bankwana da kasashen kungiyar EU.

https://p.dw.com/p/3X4fY
Protest London Brexit
Hoto: Reuters/T. Melville

Birtaniya dai ta kasance kasa ta farko da ta ware daga kasashe 28 mambobin kungiyar ta EU tun shekara ta 1973. Firaminista Boris Johnson ya jima da goyon bayan aniyar kasar ta ficewa daga kungiyar tun a shekara ta 2016 lokacin kaddamar da kuri'ar ficewar kasar. Al'amarin dai tun a baya ya haifar da rarrabuwar kai da mabanbantan ra'ayoyi, inda a yanzu haka ma Firaminista Johnson din ya daukar wa al'ummar kasar alwashin ingantacciyar makoma.

Gwamnatin Birtaniya ta umarci takaita bukubuwan farin cikin ficewar kasar daga EU domin karrama da dama daga cikin al'ummar kasar wadanda suke kyamar wannan mataki da kuma wadanda suke fargabar makomar kasar ta Birtaniya a nan gaba.