Birtaniya na yaki ne da masu alaka da al-Qaida, inji Gordon Brown | Labarai | DW | 01.07.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Birtaniya na yaki ne da masu alaka da al-Qaida, inji Gordon Brown

´Yan sanda a Birtaniya sun kai samame a gidaje da dama dake kusa da birnin Glasgow da kuma tsakiyar Ingila inda suka kame mutum na biyar a yayin da aka tsananta farautar wadanda ke da hannu a harin da aka kaiwa filin jirgin saman yankin Scotland da kuma yunkurin kai harin bama-bamai a London. A cikin wata hira da aka yi da shi ta telebijin FM Birtaniya Gordon Brown ya ce a bayyane ya ke cewa suna yaki ne da mutanen dake da alaka da kungiyar al-Qaida.

O-Ton Brown:

“Ya zama wajibi mu zama masu lura a kullum. Dole ne kuma mu kasance cikin shiri ko da yaushe. Sakon da ya kamata ya fito daga al´umar Birtaniya dai guda daya ne wato ba zamu saduda ba ba kuma zamu yarda a tursasa mana ba kuma ba zamu bari wani yayiwa tsarin rayuwar mu zagon kasa ba.”