1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Burin Birtaniya kan Afirka bayan ta fice daga EU

Usman Shehu Usman GAT
January 30, 2020

A daidai lokacin da shirin Birtaniya na ficewa daga EU a ranar 31 ga watan Janeru ke cika, kasar ta jaddada aniyarta na karfafa huldarta musamman a fannin kasuwanci da kasashen nahiyar Afirka.

https://p.dw.com/p/3X48s
England Brexit-Vertrag Unterzeichung Boris Johnson
Hoto: picture-alliance/dpa/A. Parsons

Aski ya zo gaban goshi a shirin Birtaniya na ficewa daga Kungiyar Tarayyar Turai inda a ranar Juma'a 31 ga wannan watan na Janairu kasar ke kammala shirin ficewar a hukumance. Kasar dai ta nuna ba ta da matsala a game da makomarta musamman da nahiyar Afirka bayan ta fice daga kungiyar ta EU. 

 

A bana Firaministan Britaniya Boris Johnson ya kaurace wa babban taron tattalin arzikin duniya da ya gudana a birnin Davos na kasar Switzerland domin mayar da hankali ga shata makomar dangantakar tattalin arziki da Afirka. Taron saka hannun jari da Britaniyar ta shirya a birnin Landan ya sami halartar shugabanin kasashen Afrika da dama, taron da kuma a lokacinsa Birtaniya ta jaddada sha'awarta ta yin kasuwanci da kasashen Afrika a matsayin babbar aminiyar kasuwanci. Mark-Athony Johnson shugaban kamfanin JIC ya tabbatar da hakan:

'' Dole ne Birtaniya ta lalubo wasu sabbin abokan hulda da za ta yi kasuwanci da su muddin tana son tattalin arzikinta ya dore''

UK - Africa Investment Summit 2020
Hoto: Reuters/B. Stansall

Kasancewar Birtaniyar cikin jerin kasashe na gaba-gaba masu karfin tattalin arziki a duniya kuma ta biyu a Kungiyar Tarayyar Turai, a hannu guda kasashe da dama mambobin kungiyar ta EU, na fafutukar cike gurbin da Birtaniya za ta bari musamman na abin da ya shafi alaka da nahiyar Afrika, duba da cewa nahiyar wadda ita ce ta fi kowace nahiya samun taimako daga Tarayyar Turai. Uzoamaka Madu wata kwarariya ce a kan dangantaka tsakanin kungiyar tarayyar Turai da Afrika:

'' Daga cikin masu fada a ji a kungiyar da suka hada da Jamus da Faransa za su ci gaba da kokarin kutsawa domin ya kasance su ne masu fada a ji a kungiyar idan aka zo maganar harkar da ta shafi Afrika''

Misali na baya bayan nan shi ne yunkurin Shugaba Emmanuel Macron na kasar Faransa na kokarin habbaka huldar jakadanci da kasashen Afrika kan batun samar da kudaden bai daya na ECO. Haka ma Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel, a yayin tgaron tattalin arziki a Davos ta bukaci da a shirya taro da zai tattauna abubuwa da dama da kasashen Afrika. Abin tambaya shi ne, ko menene dalilin da ya sa kasashe ma su ci-gaban tatalin arziki ke ruguguwar hada hulda da Afrika? Annie Mutamba kwararriya kan dangantakar Turai da Afirka tayi bayani tana mai cewa:

Deutschland Libyen-Konferenz in Berlin hat begonnen | Johnson und Merkel
Hoto: AFP/. T. Schwarz

'' Babban abu shi ne samun damar fada a ji a nahiyar Turai, ba wai kawai a Brassels ba, a ko'ina na hahiyar''

Duk da karakainar da manyan kasashen duniya ke yi a nahiyar Afrika ta fuskar kulla dangantakar kasuwanci ko ci-gaban kasashen, har yanzu babu wani abin a zo a gani sai tarin kalubale da kasashen na Afrika ke kara tsunduma ciki wanda hakan ke sa al'ummar kasashen kasa tantance alfanun alakar nahiyar da EU din. Haka zalika duk da zargin da ake yi wa Birtaniyar na laluben makoma bayan ta fita daga EU, wasu daga cikin kasahen Afrika sun fara ba da kai bori ya hau. Ficewar ta Birtaniya daga Kungiyar EU na zama manuniyar cewa za'a kara samun kasashe masu karfin fada a ji a duniya kasancewar za ta fara cin gashin kanta a hukumance.