1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

May ta kasa samun amincewar Majalisa kan Brexit

Abdullahi Tanko Bala
April 2, 2019

'Yan majalisar dokokin Birtaniya sun sake yin fatali da wasu shawarwari hudu na ficewar kasar daga kungiyar EU da Firaministar kasar Theresa May ta gabatar.

https://p.dw.com/p/3G483
Großbritannien London Jeremy Corbyn spricht vor Theresa May im Unterhaus
Hoto: picture-alliance/PA Wire/House of Commons

Yan majalisar sun yi watsi da dukkan shawarwarin hudu ne wadanda kakakin majalisar John Bercow ya zabo a wani yunkuri na yneman masalaha ga kiki-kakar da aka shiga kan ficewar Birtaniyar daga kungiyar tarayyar Turai EU.

Gwamnatin Birtaniyar dai na da nan da ranar 12 ga wannan Afrilu ta yanke shawara kan yadda ta ke so ta fice daga kungiyar ta EU.

Majalisar ta yi watsi da shawarar cewa Birtaniya ta cigaba da kasancewa cikin kasuwar bai daya yayin da a waje guda kuma za ta cigaba da shawarwari da kungiyar tarayyar Turai kan kawancen shige da fice na kwastam.

Kawancen kwastam na nufin cewa Birtaniya za ta cigaba da huldar kasuwanci da kungiyar tarayyar Turai ko da bayan ta fice daga kungiyar sannan za ta cigaba da bada nata kason kudi ga kasafin kudin tarayyar Turai.

Shugaban hukumar Tarayyar Turai Jean-Claude Juncker ya soki kwan gaba kwan baya da Birtaniya ke yi kan batun na Brexit yana mai cewa bai dace da 'yan siyasar Birtaniyar ba.