1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar dokokin Birtaniya ta koma zaman muhawara

Mohammad Nasiru Awal
September 25, 2019

Dawowar majalisar ta biyo bayan hukuncin kotun kolin kasar ce wadda ta dage hutun dole da Firaminista Boris Johnson ya tura majalisar.

https://p.dw.com/p/3QFwO
UK Brexit | Parlament
Hoto: AFP/HO

Shi dai Johnson ya ba da umarnin tafiya hutun na dole ne don kashe bakin majalisar a muhawarar da ake yi game da ficewar kasar daga kungiyar tarayyar Turai. Tun gabanin wannan hutu dai majalisar ta kafa wata doka da za ta hana Firaminista Johnson aiwatar da matakinsa na fitar da Birtaniya daga EU ba tare da yarjejeniya ba.

'Yan majalisar dokokin Birtaniya sun koma zaman majalisar suna masu huce takaicinsu dangane da yunkurin Firaminista Boris Johnson na dakatar da aikin majalisar da bai yi nasara ba, suna masu gargadin cewa tsarin dimukuradiyya kansa na fuskantar barazana daga gwamnati.

Manyan jami'an gwamnatin Firaminista Johnson sun tattauna da 'yan majalisa daga dukkan jam'iyyun siyasa a rana ta farko bayan hukuncin kotun kolin Birtaniya da ya ayyana matakin firaminista na dakatar da majalisar tsawon makonni biyar da cewa haramun ne domin ya kawo cikas ga mahawarar da ake yi dangane da ficewar Birtaniya daga kungiyar tarayyar Turai EU da ake wa lakabi da Brexit.

Großbritannien London | Wiederaufnahme der Parlamentssitzung
Wasu 'yan majalisar dokokin BirtaniyaHoto: picture-alliance/AP Photo/House of Commons/J. Taylor

Sai dai a jawabin da ya yi a gaban wakilan majalisar babban lauyan gwamnati Geoffrey Cox ya zargi majalisar da zama wani abin kunya, inda ya kare shawarar da ya ba wa Johnson yana mai goyon bayan matakin dakatar da aikin majalisar.

“Ya ce bana jin zan shiga wani kace-nace da 'yan adawa. Idan suna ganin wannan gwamnati ba za ta iya mulki ba to su fada wa shugabansu ya gabatar da kudurin kada kuri'ar yanke kauna. A shirye muke mu hadu da shi a duk inda yake so a kuma gaban masu zabe."

Shi dai babban lauyan gwamnati ya mayar da martani ne ga wasu kalamai da dan jam'iyyar Labour Barry Sheerman ya yi inda ya caccaki Firaminista Johnson.

“Ya ce na zo majalisa ne don na yi wa babban lauyan gwamnati jaje, amma kalaman da ya furta ba su dace ba musamman bisa la'akari da yadda gwamnati ta so ta juya alakar wannan majalisa. Hakan ba zai yiwu ba ga wannan majalisa da ta ginu bisa tsari na dimukuradiyya. 


Ita ma shugabar jam'iyyar adawa ta Liberal Democrat Jo Swainson ta zargi Firaminista Johnson da karya dokokin dimukuradiyya, tana mai cewa mutum wanda ba za a iya yarda da shi ba.

UN-Klimagipfel New York 2019 | Boris Johnson, Premierminister Großbritannien
Firaministan Birtaniya Boris JohnsonHoto: Reuters/S. Stapleton


"Majalisa za ta koma bakin aiki abu ne mai matukar muhimmanci ga tsarinmu na dimukuradiya. Firaministnamu ya ci zarafin dimukuradiyyarmu, an same shi da laifin karya doka, da katse aikin majalisa ba bisa ka'aida ba saboda haka shi da kanshi na zama hujjar cewa ba za a iya yarda da shi ba."

Ganin yadda ya sha kaye a kotun kolin Birtaniya, masana harkoki siyasa a Biratniya sun ce babu alamar cewa Firaminista Johnson zai bukaci Sarauniyar Ingila Elizabeth ta biyu ta sake dakatar da aikin majalisa domin hakan ka iya zama babban abin kunya.
 

Tsallake zuwa bangare na gaba Rahotanni da Sharhuna

Rahotanni da Sharhuna