Jam'iyyar Labour a Birtaniya za ta shiga zabe
October 29, 2019Shugaban jam'iyyar Labour a Birtaniya Jeremy Corbyn ya tabbatar cewa jam'iyyarsa ta hamaiya ta janye adawar da take ga gudanar da sabon zabe na gaba da wa'adi, bayan da Kungyar Tarayyar Turai ta ba da karin lokaci na watanni uku kan ficewar Birtaniya daga kungiyar.
Corbyn ya ce za su yi nasara a zaben da bisa ga dukkan alamu zai gudana cikin watan Disamba mai zuwa.
Ya ce: "Mun shirya mu yi zabe. Za mu fita da gagarumin sako yadda za mu canja al'ummarmu don kawo karshen rashin daidaito da rashin adalci. Za mu tinkari matsalar talauci da da yawa daga cikin mutane ke fuskanta. Lalle muna son zaben, amma kuma muna son a cire maganar ficewar Birtaniya daga EU ba tare da yarjejeniya ba."
Ita dai jam'iyyar Conservative ta Firaministan Birtaniya Boris Johnson na son a gudanar da sabon zabe a ranar 12 ga watan Disamba na wannan shekara ta 2019.