Birtaniya: Jam'iyyar Conservative ta yi nasara a zabe
December 13, 2019Talla
Jim kadan bayan bayyana sakamakon wasu mazabun, jagoran adawa Jeremy Corbyn ya bayyanawa magoya bayansa cewar ba zai shugabanci jam'iyyar ba a zabe na gaba, yayin da firaminista Johnson ya kara jaddada aniyar ganin kasar ta Birtaniya ta kammala ficewa daga Kungiyar EU.
Tuni dai 'yan jam'iyyar ta Conservartive suka fara taya juna murnar wannan nasara da suka samu. Haka ma abin yake ga shugaban Amirka Donald Trump, wanda ya shiga sahun gaba na shugabannin duniya da suka aikewa Firaminista Boris Johnson din sako na taya shi murna kan lashe zaben na jiya Alhamis.