Birtaniya da Jamus za su karbi bakoncin taron tallafa wa Siriya a 2016 | Labarai | DW | 16.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Birtaniya da Jamus za su karbi bakoncin taron tallafa wa Siriya a 2016

A shekara mai kamawa ta 2016 gwamnatocin Birtaniya da Jamus za su shirya babban taron tara kudaden tallafa wa Siriya mai fama da yakin basasa.

Shugabannin kasar Birtaniya da Jamus sun ce za su gudanar da wani taro a farkon shekara mai zuwa don tara kudin tallafi ga 'yan Siriya da yakin kasar ya daidaita, wadanda kuma ke cikin halin kuncin rayuwa. A lokacin da suke magana a gefen taron kungiyar kasashe masu tagomashin tattalin arziki na G-20 a kasar Turkiyya, kasashen Jamus da Birtaniya sun ce tallafin da ake samu daga kasashen duniya ya ragu matuka. Yakin basasar Siriya ya haddasa matsalar 'yan gudun hijira mafi muni a Turai tun bayan yakin duniya na biyu. Miliyoyin 'yan kasar sun rasa muhallansu yayin da kimanin dubu 250 suka mutu a yakin tsakanin dakarun gwamnati da na kungiyoyin 'yan tawaye ciki har da kungiyar IS mai da'awar kafa daular Musulunci a Iraki da Siriya.