1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Birtaniya da Faransa na son rage kwarar bakin haure

November 14, 2022

Kasashen Birtaniya da Faransa za su sanya hannu kan wata yarjejeniyar don rage yawan kwarar bakin hauren da ke tsallakawa zuwa kasashen Turai.

https://p.dw.com/p/4JTCt
Ministar cikin gida ta Birtaniya Suella Braverman
Hoto: Amanda Rose/Avalon/Photoshot/picture alliance

Ministan cikin gida na Faransa Gerald Darmanin zai karbi bakuncin takwararsa ta Birtaniya Suella Braverma a birnin Paris don sanya hannu kan yarjejeniyar ta kara jami'an da ke rika sintiri a tekunan kasashen.

Birtaniya dai ta ce za ta kara kudin da ta ke bai wa Farasan a duk shekarar zuwa dala miliyan 71 domin magance matsalar.

Alkalumma sun yi nuni da cewa fiye da mutane dubu 40 ne suka yi amfani da kwale-kwale wajen tsallakawa zuwa kasashen Turai a cikin wannan shekarar, lamarin da ya sanya sabon Firanministan Birtaniya Rishi Sunak ke fuskantar matsin lamba don samar da hanyar da za a rage kwarar bakin haure.