Birtaniya da batun ci gaba da zama a EU | Labarai | DW | 03.02.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Birtaniya da batun ci gaba da zama a EU

Shugaban hukumar Tarayyar Turai Jean-Claude Juncker ya nuna goyon bayansa dangane da batun tattaunawa kan ci gaba da kasancewar Birtaniya cikin kungiyar ko kuma akasin haka.

Firaministan Birtaniya David Cameron da Jean-Claude Juncker shugaban hukumar EU

Firaministan Birtaniya David Cameron da Jean-Claude Juncker shugaban hukumar EU

Junker ya bayyyana cewa matakin amincewa da tattauna batun da shugaban kungiyar ta Trayyar Turai wato EU Donald Tusk ya dauka, na zaman wani mataki na yin adalci ga Birtaniya da kuma sauran kasashe 27 da ke zaman mambobin kungiyar ta EU. Junker ya kara da cewa:

"A jiya Shugaba Tusk ya gabatar da kudiri kan sabuwar hanyar da ya kamata a bi kan ci gaba da kasancewar Birtaniya cikin kungiyar EU. Hukumar Tarayyar Turai na da hannu cikin samar da wannan sabon kudiri domin nemo mafita. Kullum ina jaddada cewa ina son Birtaniya ta ci gaba da kasancewa cikin Tarayyar Turai, amma bisa adalci. Wannan sabon kudiri ya yi adalci ga Birtaniya da sauran kasashen kungiyar 27 da kuma majalisar Tarayyar Turan."