Birnin Hébron ya shiga tarihi | Labarai | DW | 07.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Birnin Hébron ya shiga tarihi

Hukumomin Falasdinu sun ce sun samu  babbar nasara  bayan da hukumar ilimi da raya al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya UNESCO ta amince da wani kudirin na kare birnin Hébron wanda Isra'ila ta mamaye.

Ministan harkokin waje na Falasdinu ya ce saka birnin na Hébron a jerin birane masu kayan tarihi na duniya wata nasara ce ta diplomasiya da suka cimma a kokarin da suke ne samun yanci. Manbobi 12 na Hukumar ta UNESCO suka kada kuri'ar a Poland  yayin da shida suka kaurace, kana uku kuma suka hau kujerar naki.